Gwamnatin Tarayya ta amince da sabon tsarin karin albashi ga jami’an rundunonin sojin Najeriya, inda wasu jami’ai za su samu karin kashi 30 zuwa 80 cikin 100.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da karin albashin da zai amfani kusan jami’an tsaro 250,000 a fadin kasar.
Sabon karin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2026, inda jami’an da ke sama da mukamin Kanal (Colonel) za su samu karin kashi 30 cikin 100.
- Kotun Tarayya ta yi watsi da bukatar jam’iyyar NDC kan cancantar ‘Yan Takara a Dokar Zaɓe
- Majalisar Dattawa ta gayyaci CBN, NDDC da NUPRC bayan sun ƙi halartar zaman binciken rahoton NEITI
- Majalisar dokokin kano ta amince da kudirin takaita ƙarin kuɗi a makarantu masu zaman kansu
Wadanda suke daga mukamin Kanal zuwa Warrant Officer za su samu karin kashi 50 cikin 100, yayin da jami’an da ke daga Private zuwa Staff Sergeant za su samu karin kashi 80 cikin 100.
A cewar sanarwar Fadar Shugaban Kasa da mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, sabon tsarin zai kara kudin albashin sojojin Najeriya na shekara daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.
Shugaba Tinubu ya ce karin albashin wani bangare ne na kokarin gwamnati na inganta walwalar jami’an tsaro da kuma kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro suna fuskantar kalubale wajen yaki da ta’addanci da‘yan bindiga da garkuwa da mutane a sassan kasar, don haka suke bukatar kulawa da tallafi.
Tinubu ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa tsaro muhimmanci tare da samar da makamai da fasahohin zamani domin taimakawa rundunonin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Ya kuma bukaci jami’an sojin kasar da su dauki wannan karin albashi a matsayin nuna godiya bisa irin sadaukarwar da suke yi wa kasa.