Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da ke da nufin daidaita yadda makarantu masu zaman kansu ke ƙara kuɗin makaranta tare da ƙarfafa sa ido kan gudanar da harkokin ilimi a jihar.
Kudirin, da aka yi wa laƙabi da Kudirin Gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai na Jihar Kano, 2026, ya samu amincewar majalisar ne a ranar Litinin bayan kammala karatu na uku da kuma tattauna shi a zaman majalisa.
Da yake magana bayan amincewa da kudirin, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ya ce duk wata makarantar firamare ko sakandare mai zaman kanta dole ne ta fara tattaunawa da Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) kafin ta ƙara kuɗin makaranta.
- Shettima ga jihohi –ku rinƙa gogayya wajen haɓaka tattalin arziki
- INEC ta wallafa sunayen ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na 2027
- Sojoji sun daƙile harin ‘yan ta’adda a Kasuwar Daji, sun ceto mutane 9
Ya ƙara da cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta da aka amince da shi ba zai wuce kashi 10 cikin 100 na kuɗin makarantar da ake bi a halin yanzu ba.
Kudirin, wanda yanzu ke jiran sa hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf kafin ya zama doka, ya kuma tanadi cewa Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai dole ne ya kasance ƙwararren masani a fannin ilimi ko kuma ma’aikacin ilimi da ya kai aƙalla Matsayi na 14 a aikin gwamnati kuma yayi ritaya.
Lawan Hussaini ya kuma bayyana cewa daga yanzu ba za a bar makarantu masu zaman kansu su karɓi kuɗin rajistar jarabawa daga ɗalibai fiye da kashi 10 cikin 100 na kuɗin da hukumomin shirya jarabawa irin su WAEC, NECO da NBTE suka kayyade ba.
Har ila yau, kudirin ya rage kuɗaɗen harajin doka da makarantu masu zaman kansu ke biya wa hukumar daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 5 cikin 100.
A cewar Lawan Hussaini, waɗannan gyare-gyaren na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta gudanar da makarantu masu zaman kansu da kuma ɗaga darajar ilimi a faɗin Jihar Kano.