Mai karbar bakuncin Gasar cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON), Moroko da Algeriya sun kai wasan Kwata-fainal bayan kammala wasannin Rukuni na A a daren ranar Litinin, yayin da Senegal da Kenya suka fice daga gasar.
Moroko sun tashi kunnen doki 0-0 da Senegal a filin wasa na Olympic Stadiya da ke Rabat. Wasan ya kasance mai cike da tashin hankali saboda abin da ya faru na bugun fenareti.
An baiwa Atlas Lionesses bugun fenareti, inda Yasmin Mrabet ta buga amma mai tsaron ragar Senegal, Adji Ndiaye, ta kama, sai dai Alkalin wasa ya umarci da a sake bugawa bayan ya ce mai tsaron ragar ta fice daga layinta kafin a buga fenaretin.
- Glasgow 2026: Najeriya ta zo ta 7 da lambobin yabo 24 a Gasar Commonwealth
- WAFCON: Yadda Super Falcons ta doke Zambia duk da samun jan kati
- Zaben NFF: Za a fara sayar da fom ranar Asabar 1 ga Agusta
Daga baya, Moroko sun yi kokarin sauya wadda za ta sake bugawa, yayin da kyaftin din su, Ghizlane Chebbak, ta shirya zata buga sai Alkalin wasa ya ce dole sai dai Mrabet ce za ta sake bugawa. Ndiaye ta sake kamawa. Da haka aka tashi 0-0 a wasan.
Duk da kunnen dokin, maki 4 da Senegal ta tara bai isa ta tsallake zuwa matakin gaba ba. Teranga Lionesses masu matsayi na 79 a duniya sun fice a matakin rukuni, duk da sun kai Kwata-fainal a 2022 da 2024.
Wannan sakamako ya kara tsawaita tarihin Senegal na rashin nasara a kan Moroko domin a cikin karawa 7 tsakanin su, ba su taba cin nasara ko zura kwallo ba.
A daya wasan na Rukuni A, a filin wasa na Moulay Abdellah, Algeriya ta doke Kenya da ci 2-0. Da wannan ne ta samu tsallakawa zuwa matakin gaba.
Marine Dafeur ta fara zura kwallo a minti na 13, kafin Lynda Bendris ta kara ta biyu a minti na 22, ta haka Fennecs suka samu nasara mai sauki.
Wannan shan kaye ya kawo karshen kokarin Kenya ba tare da samun wani maki ba. Harambee Starlets masu matsayi na 128 a duniya suma sun fice a matakin rukuni kamar yadda suka yi a WAFCON na 2016.
Algeriya masu matsayi na 74 a duniya kuma suna buga gasar karo na 7, sun kai Kwata-fainal karo na biyu kenan, dai-dai da kokarin da suka yi a 2024.
Kasar Moroko ce ke saman teburin Rukunin A da maki 7, inda suka ci kwallo 5, kuma ba a ci su ko kwallo guda ba. Algeriya na matsayi na biyu da maki 6. Sun ci kwallo 4, an ci su 1. Senegal ta na da maki 4, yayin da Kenya bata da maki 0, kuma ba su ci kwallo ba, amma an ci su 7.