Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana goyon bayansa ga gasar haɓaka tattalin arziki tsakanin jihohi 36 na tarayyar Najeriya, yana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen cimma burin ƙasar na samun wadata, bunƙasar tattalin arziki, kare martabar al’umma, da samar da guraben aikin yi.

Shettima ya bayyana hakane yayin da yake jawabi a Taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Jihar Delta na shekarar 2026 da aka gudanar a Asaba, Jihar Delta.

Ya ce wajibi ne kowace jiha ta tsara hanyar bunƙasa tattalin arzikinta bisa tarihinta, yanayin ƙasarta, al’ummarta, da kuma irin fa’idodin da take da su.

A cewarsa, ƙarfin Najeriya ba ya ta’allaka ga gwamnatin tarayya kaɗai, sai dai yana cikin yadda gwamnatocin jihohi ke ƙoƙarin jawo masu zuba jari da bunƙasa tattalin arzikinsu.

Ya kuma jaddada cewa lokaci ya yi da jihohi za su daina takaita kansu ga tattara bayanan kadarori kawai, su mai da hankali kan aiwatar da ayyukan ci gaba da samar da guraben aikin yi ga al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *