Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana damuwarta kan yadda babu wata jiha da ta shiga gasar Naira miliyan 50 na gwamnatin tarayya, domin ƙarfafa musu gwiwar gyaran guraren da aka yi watsi da su.
- Remi Tinubu ga Saudiyya: Ku taimaka don tsara Ilimin Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta
-
Oluremi Tinubu ta bai wa ɗakunan karatu na makaranatun Gwamnati littattafai 140, 000
Ta bayyana hakan ne a wajen taron karrama Hukumar Babban Birnin Tarayya saboda nasarorin da ta samu a fannin kula da muhalli ƙarƙashin shirin *Renewed Hope Green Initiative.
Remi Tinubu ta bukaci gwamnatocin jihohi su bai wa matasa dama su shiga shirye-shiryen kare muhalli tare da amfani da tsare-tsaren da gwamnati ta tanada domin inganta muhalli.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce duk da ware kyautar Naira miliyan 50 domin ƙarfafawa jihohi gwiwar gyara guraren da aka yi watsi da su, babu wata jiha da ta nuna shaawa,
Ta kuma yaba wa Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, bisa yadda ya sauya fasalin City Gate, tana mai cewa abin akwai burgewa matuƙa.