Uwargidan Shugaba Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta raba kayan tallafi ga  wasu masu kananan sanao’i su dubu 1 a yankin Karon Majigi dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

Cikin wani sako da Karamar ministar Babban Birnin Tarayya Mariya Mahmood Bunkure ta wallafa a shafinta na Facebook, ta yaba wa Uwargidan shugaban bisa irin wannan kokarin da takeyi na tallafawa masu karamin karfi

Mariya Bunkure ta bayyana aikin da cewa yana cikin shirin sabunta fata da gwamnatin Shugaba Tinubu ta bullo dashi, domin samar da walwala da karfafa tattalin arzikin yan kasa

Tallafin, wanda Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ta shirya ta ƙarƙashin Shirin (Renewed Hope Initiative, RHI), ya samar da tallafin kuɗi da kayan aiki ga kananan ‘yan kasuwa  1,000, da aka zaɓo daga ko’ina cikin Babban Birnin Tarayya Abuja.

A baya bayan nan Uwargidan Shugaban kasar na sanya ido tare da bibiyar wasu daga cikin manufofi raya al’umma da Gwamnatin Tarayya ke da muradin cimma kafin karshen wa’adin mulkin ta, domin tabbatar da aiwatar dasu.

Sai dai Masharhanta na ganin akwai alamun kurewar lokaci, ganin yadda kakar manyan zabukan kasar ke karatowa gada-gadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *