Dakarun Sashen 2 na Operation FANSAN YAMMA sun daƙile wani yunƙurin da ‘yan ta’adda suka yi na kutsawa cikin Forward Operating Base (FOB) da ke Kasuwan Daji, Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda ta Jihar Zamfara, inda suka kashe da dama daga cikin maharan tare da ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya fitar ta ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar ranar 2 ga Agustan 2026, lokacin da ‘yan ta’addan suka yi ƙoƙarin amfani da duhun dare domin kutsawa cikin sansanin sojoji.

A cewar sanarwar, dakarun da ke bakin aiki sun gano motsin maharan cikin lokaci, inda suka buɗe musu wuta tare da tilasta musu janyewa.

Bayan fafatawar farko, an tura ƙarin dakaru domin bin sawun ‘yan ta’addan da suka tsere. A yayin harin, maharan sun yi garkuwa da wasu mazauna yankin, amma bibiya da dakarun suka yi ta kai ga ceto mutane tara cikin ƙoshin lafiya.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa wani jami’in Sojin Najeriya da kuma wani jami’in Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da maharan.

Haka kuma, sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka kwashe su ta jirgin sama zuwa cibiyar lafiya domin ci gaba da samun kulawa.

A halin yanzu, an bayyana cewa suna cikin yanayi mai kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *