Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) ta shigar, wadda take ƙalubalantar tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta shekarar 2026 game da cancanta ko rashin cancantar ‘yan takara.
A zamanta na ranar Talata, Mai Shari’a Muhammed Umar ya bayyana cewa ƙarar mai lamba ba ta da wani tasiri ko tushe a Shari’ar.
Mai Shari’ar ya ce sassan dokar da jam’iyyar ke ƙalubalanta na cikin manyan ginshikan dasuka gina Tsarin Mulki ne na shekarar 1999.
- Za mu dakatar da hare-hare a Iran bayan an cimma wasu ka’idojin yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin—Trump
- Ba mu da isasshen ƙarfi da za mu kare Isra’ila daga hare haren Iran – Janar Alexus
- Mali: HRW ta zargi dakarun Africa Corps na Rasha da kashe fararen hula takwas
Jam’iyyar ta NDC ta shigar da ƙarar ne a kan Babban Lauyan Tarayya (AGF), Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Hukumar Zaɓe (INEC).
A cikin buƙatun ta, NDC ta nemi kotun ta bayyana Sashe na 138 da na 77(5) na Dokar Zaɓe ta 2026 a matsayin waɗanda suka saba wa tsarin mulki.
Haka kuma, ta buƙaci kotun ta amince cewa ana iya ci gaba da ƙalubalantar cancantar ɗan takara ko da bayan an gama zaɓe da bayyana nasara.
Sai dai kuma, Mai Shari’a Umar ya amince da ƙorafe-ƙorafen farko da masu kariya suka gabatar kan rashin dacewar salon sigar shigar da shari’ar, yana mai cewa mai ƙarar na ƙoƙarin jan hankalin kotun ne ta yi fassara kan tanade-tanaden doka da tsarin mulki da suka riga suka bayyana.