Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta ce ta gano bindigu biyu kirar FN FAL da harsasai masu yawa yayin wani sumame da jami’anta suka kai a wata maboyar da ake zargin ‘yan bindiga ke amfani da ita a dajin Dajin Madam, dake kan iyakar jihohin Filato da Bauchi.

Mai Magana da yawun  ‘yan sanda Josephine Adeh, ta bayyana cewa jami’an rundunar sun kai sumamen ne sakamakon bayanan sirri da suka samu daga wani da suka kama, bisa zargin aikata manyan laifuka.

“A halin yanzu wanda ake zargi yana hannunmu, kuma shi ne ya kai jami’anmu zuwa wurin- Sai dai ba mu samu mutumin da ya ce zai nuna mana ba. Bayan mun binciki yankin, mun gano bindigogi biyu. Binciken zai ci gaba domin samun ƙarin bayanai daga wajen wanda ake tsare da shi da kuma kamo sauran waɗanda ke da hannu a lamarin,” in ji ta.

Adeh ta ƙara da cewa jami’an Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane na rundunar sun gudanar da aikin ne a ranar 2 ga Agusta, bayan samun sahihan bayanan sirri daga ɗaya daga cikin mutanen da aka kama.

A cewar ta, bayanan sirrin sun jagoranci jami’an zuwa cikin dajin, inda ake zargin maboyar masu aikata laifuka ce.

Ta tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukanta, tare da ci gaba da sintiri da bincike har sai an kamo dukkan mambobin ƙungiyar tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *