Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta gudanar da wannan jawabi ga jama’a domin bayyana dalilan matakin kariya da ta dauka na toshe asusun banki na gwamnatin jihar Osun, ba tare da la’akari da zaben gwamna da ke tafe a jihar ba.
Hukumar ta kasance tana binciken gwamnatin jihar Osun tun watan Maris na shekarar 2026, game da zargin tafka magudi da almundahana da kudaden kariya daga matsalolin fari da ambaliya (Ecology Funds), kudaden agaji da tallafi (Intervention Funds), da kuma asusun rabon kudaden shiga na tarayya (FAAC) da suka kai jimillar N11,000,000,000 (Biliyan Goma sha Daya na Naira). Don haka, wasu jami’an gwamnatin jihar, musamman babban akanta na jihar (Accountant General), sun riga sun gana da masu bincike na EFCC.
Wadannan bincike da ake gudanarwa a halin yanzu a kan gwamnatin jihar ba za su sa a sanya dokar hana fitar da kudi (Post No Debit) a asusun ba, sai dai saboda yunkurin kwashe kudaden cikin gaggawa da bai dace ba zuwa wasu asusun ajiya daban-daban masu zaman kansu da ake zargi tun ranar 2 ga Agusta, 2026.
Hukumar ta lura da tura makudan kudade zuwa kamfanoni daban-daban, wanda hakan ya sa ta dauki matakin gaggawa na dakatar da wannan lamari ta hanyar toshe asusun da ake kwashe kudaden daga ciki.
Aikin EFCC na rigakafin barna tsari ne da aka samar domin kare kudaden al’umma, kadarori, da albarkatun kasa.
Hukumar ba za ta zuba ido tana kallo ana yi wa asusun gwamnatin jiha fashi ba. Yayin da hukumar ke da cikakkiyar masaniya kan zaben gwamna da ke tafe a jihar Osun, tana da alhakin yin aiki domin kare mutuncin kudaden jihar. Ba zai zama adalci ga hukumar ba idan ta yi amfani da uzurin zabe mai zuwa domin ta nade hannayenta ba tare da gudanar da ayyukan da doka ta ba ta ba.
Haka zalika, yana da kyau a bayyana cewa hukumar tana sanya idanu kan kudaden sauran jihohi kamar jihar Osun. Jihohi da dama suna karkashin binciken hukumar domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Hukumar ta dade tana jaddada cewa ba ta bangaranci ko nuna bambanci, a ko da yaushe tana aiki ne don amfanin ‘yan Najeriya baki daya. An toshe asusun gwamnatin jihar Osun ne domin ceton kudaden al’umma daga handama da yayatawa.
Ana bukatar jama’a da su yi watsi da labaran kanzon kurege da gangan da ake yadawa domin bata sunan ayyukan EFCC. Bukatun daukacin ‘yan Najeriya sun fi komai girma, kuma hukumar za ta ci gaba da kare su a koda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *