Cristiano Ronaldo, dan wasan gaba na Portugal da Al Nassr.

Cristiano Ronaldo ya kalli wasan sada zumuntar da Al Nassr ta sha kaye a hannun ƙungiyar ƙasar Spaniya dake buga Gasar mataki na 2, wato UD Almeria wadda ya mallaki hannun jarin ta da kaso 25, a ranar Talata, a Lisbon.

Ɗan wasan gaba na Portugal ya kalli wasan daga wurin da masu kallo ke tsayuwa, sannan bayan an tashi ya gaisa da abokan wasansa na Al Nassr. Almeria ce ta lashe wasan da ci 2-0.

Ronaldo mai shekara 41 an gan sa yana rungumar kocin Al Nassr Ange Postecoglu, wanda ya maye gurbin Jorge Jesus.

Bayan wasan, shugaban UD Almeria Mohamed Al Khereiji ya bai wa Ronaldo riga ta musamman da aka rubuta a gabanta “Ronaldo ONE OF US”.

Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau 5 ya saka hannun jari a Almeria ta hanyar kamfaninsa CR7 Sports a watan Fabrairu.

Wasan na ranar Talata shi ne wasan sada zumunta na ƙarshe ga Al Nassr kafin su fara kare kambun Gasar Saudi Pro-League da Al-Fateh a ranar 15 ga Agusta.

Ronaldo na ci gaba da hutu tun bayan da Portugal ta fice a hannun Spaniya a zagaye na 16 na Gasar Cin Kofin Duniya a ranar 6 ga Yuli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *