Chelsea ta sha kaye da ci 1-0 a hannun Juventus a wasan sada zumunta da suka buga ranar Laraba, a Hong Kong.

Duk da kyawawan bajekolin da wasu sabbin ‘yan wasan da Chelsea ta sayo a bazara suka nuna, hakan bai hana su yin rashin nasara ba.

Xabi Alonso ya yanke shawarar farawa da ɗan wasan gaba, Danny Welbeck, tare da Geovany Quenda a gefen dama. Dukkannin su biyun sun nuna alamun samar da dama a rabin farko wanda aka tashi ba tare da an ci ƙwallo ba.

Quenda da mai tsaron baya na bangaren dama, Marco Palestra, sun fahim ci junan su sosai, wanda hakan zai iya taimakawa Alonso da zarar an fara kakar wasa.

Ɗan wasa Edon Zhegrova ne ya zura ƙwallon da ta baiwa Juventus nasara yayin fafatawar da ta bar Alonso amsa tambayoyi da dama da zai amsa a wasa na gaba.

Wasannin sada zumunta 3 da suka rage wa Chelsea kafin su fara gasar Firimiyar Ingila ranar 24 ga Agusta sune kamar haka:

Asabar: da AC Milan a Indonesia

Lahadi: da Johor Darul Ta’zim a Malaysia

15 Agusta: da Real Sociedad a Stamford Bridge

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *