Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta bayyana cewa binciken farko da ta gudanar ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta taɓa naɗa Adeniyi Adeyemi Matthew a matsayin Darakta Janar na wata Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Ƙasa (PFIPC) da ake zargi ta bogi ce ba, tare da cewa takardar naɗin aikin da ya riƙa nunawa jabu ce.
Shugaban ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu (SAN), ne ya bayyana hakan bayan miƙa rahoton binciken farko ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kwanaki 30 bayan shugaban ƙasar ya ba hukumar umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
A cewar sa, binciken ya gano cewa ba a taɓa kafa hukumar PFIPC bisa doka, umarnin shugaban ƙasa ko wata sahihiyar takardar gwamnati ba.
- ‘Yan sanda sun kama mutum biyar kan raba maganin gargajiya ba tare da izini ba a Kano
- ‘Yan Sanda sun gano maboyar ‘yan bindiga akan iyakar Filato da Bauchi
Ya ƙara da cewa Adeyemi ya yi amfani da takardun bogi wajen gabatar da kansa a matsayin shugaban hukumar, tare da kwaikwayon tsohuwar hukumar PEAC da kuma amfani da ofisoshi da takardun gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban ICPC ya ce binciken ya kuma gano cewa Adeyemi ya ƙirƙiri wasu ƙarin hukumomi biyu na bogi domin gudanar da ayyukansa ba bisa doka ba, inda ya yi amfani da dokokin ƙarya wajen buɗe asusun banki.
Sai dai ya jaddada cewa binciken bai gano wata shaida da ke nuna cewa an amince ko an fitar da kuɗin Gwamnatin Tarayya ga hukumar PFIPC ko PEAC ba, haka kuma bai samu wata matsala a tsarin aiki na Fadar Shugaban Ƙasa ko Babban Bankin Najeriya (CBN) ba.
ICPC ta ba da shawarar a gurfanar da Adeyemi a gaban kotu, tare da ɗaukar matakin ladabtarwa kan jami’an gwamnati da ake zargin sakacin su ya ba da damar gudanar da ayyukan hukumar ta bogi.
Hukumar ta ce binciken ayyukan Adeyemi da asusun bankunan sa, da na waɗanda ake zargin sun yi aiki tare da shi na ci gaba.