Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutum biyar da ake zargi da rarraba tare da sayar da wani maganin gargajiya ba tare da amincewar hukumomin lafiya ba.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce jami’anta da ke 52 PMF Challawa sun cafke mutanen ne a ranar 4 ga Agusta, 2026, a harabar cocin ECWA da ke bayan sansanin rundunar da ke 52 PMF Challawa, bayan samun korafe-korafen al’umma kan lamarin.

‘Yan sandan sun bayyana cewa mutanen, ƙarƙashin jagorancin Simon Gbaaondo, mai shekara 50 daga jihar Nasarawa, na bai wa jama’a maganin gargajiya kyauta tare da sayar da shi ga dimbin mazauna yankin Panshekara, ba tare da samun izini daga hukumar NAFDAC da sauran hukumomin kula da lafiya ba.

Rundunar ta ce an gayyaci mutumin da ya ba su damar gudanar da aikin a harabar cocin domin bincike, yayin da aka miƙa shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar a Kano.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargaɗi daidaikun mutane da ƙungiyoyi da su guji gudanar da rabon magunguna ko ayyukan jinya ba tare da sahalewar gwamnati da hukumomin da abin ya shafa ba, yana mai cewa hakan na iya jefa lafiyar jama’a cikin haɗari tare da kawo barazana ga tsaro.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a su rika kai rahoton duk wani shirin raba magungunan da ba a tantance ko amince da su ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *