Gobara ta tashi a daren Alhamis a Gidan mai na AY Shafa da ke bayan Rita Lori Otel dake Area 8, Garki a birnin Abuja.

Rahotannin sun nuna cewa gobarar ta fara ne da daddare, lamarin da ya haifar da tsaiko da firgici ga mazauna yankin da masu wucewa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, haka kuma babu cikakken bayani kan ko an samu asarar rayuka ko jikkata.

‘Yan sanda sun kama mutum biyar kan raba maganin gargajiya ba tare da izini ba a Kano
Mauludin Shehu Tijjani: Shugaban Darikar Tijjaniyya na duniya ya sauka Najeriya

Amma a daidai wannan lokacin jami’an kashe gobarar sun karaoke wajen.
Kuma Hukumomin da abin ya shafa za su fitar da cikakken bayani bayan an shawo kan lamarin.

Hukumar Dakile Gobara ta Fire Service ta’isa gurin domin kawo dauki, yayin da ta umur ci al’umma da suyi nesa da gidan man da abin ya auki saboda Kare rayuka da dukiyoyin al’umma, acikin wata sanar Wanda mai magana da yawun Hukumar yasawa hannu DCF P.O. Abraham, MPhil.

Blueprint Radio na ci gaba da bibiyar lamarin, kuma za ta kawo muku ƙarin bayani.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *