Kocin tawagar Flying Eagles ta Najeriya, Abdu Maikaba, ya yi imanin cewa ‘yan wasan sa suna da damar rama kayen da suka sha a hannun Burkina Faso a matakin rukuni a ranar Lahadi.

Flying Eagles, masu riƙe da kofin sau 7, za su fafata da Young Stallions ta ƙasar Burkina Faso a wasan ƙarshe na Gasar WAFU B U20 a filin wasa na Stade Charles Konan Banny da ke Yamoussoukro, a ƙasar Ivory Coast.

Burkina Faso ce ta yi nasara a wasan matakin rukuni da suka hadu, inda suka doke Najeriya da ci 2-0.

Kazalika, tawagun biyu sun tashi canjaras, wato 2-2 a wasan da suka buga a Jamhuriyar Nijar a shekarar 2022, yayin da Burkina Faso ta sake doke Najeriya da ci 1-0 a wasansu na 2024 da aka buga a Lomé.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta ce Flying Eagles, wadda ta kasance zakaran Afirka sau 7, ta na fatan kare kambun Gasar yankin da suka lashe a Lomé, dake ƙasar Togo, a watan Oktoba na shekarar 2024.

Wannan ne karo na farko da tawagun biyu za su haɗu a wasan ƙarshe na wannan gasa ta yankin, duk wasanninsu da suka gabata sun haɗu ne kawai a matakin rukuni.

Maikaba ya ce tawagarsa za ta yi amfani da darasin da ta dauka daga wasannin su na baya da Burkina Faso wajen shirya wa fafatawar na ranar Lahadi.

“Na yi imanin cewa wannan dama ce a gare mu da za mu gyara kuskuren da muka samu a baya, bayan da muka sha kashi a hannun Burkina Faso a matakin rukuni,” in ji Maikaba.

“Tun da mun taba haduwa da su, yanzu mun san yadda salon wasan su yake, kuma muna aiki akan yadda za mu yi amfani da raunin da suke da shi, tare kuma da kara karfafa karfinmu.”

Wannan wasa zai kuma tantance tawaga ta biyu daga yankin WAFU B da za ta bi sahun masu masaukin baki, wato kasar Ghana zuwa Gasar cin Kofin Kasashen Afirka na ‘yan kasa da shekaru 20 da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *