Dakarun Operation FANSAN YAMMA a Jihar Zamfara, sun tarwatsa wasu hanyoyin samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda, sun lalata wani abin fashewa (IED), tare da kama wasu mutane biyu da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda.

Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA sun gudanar da jerin ayyuka daban-daban a sassan Jihar Zamfara ranar 7 ga Agusta, 2026, inda suka samu nasarori da dama a kan ’yan ta’adda.

Ayyukan sun haɗa da dakile zirga-zirgar ’yan ta’adda da kwato kayan soji da na sadarwa da lalata wani abin fashewa IED da aka gano a wata babbar hanya, da kuma kama wasu mutane da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda wajen samun kuɗi da kayayyaki.

Dakarun sashe na 2, tare da haɗin gwiwar tawagar ’yan sandan da ke kula da abubuwan fashewa, sun mayar da martani ga rahoton wani abin fashewa da aka gano kusa da ƙauyen Jabanda, a ƙaramar hukumar Zurmi.

Dakarun sun gano abin fashewar tare da kwance shi, sannan suka binciki hanyar domin tabbatar da cewa babu sauran barazana.

A lokacin da dakarun ke dawowa daga wannan aiki, sun yi arangama da ’yan ta’adda a ƙauyen Birnin Tsaba da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji.

Dakarun sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan, inda suka tilasta musu komawa cikin daji.

Bayan haka, dakarun sun gudanar da bincike a yankin tare da kwato babura biyu da hular jeji mai launin kame-kame da rediyon sadarwa ta hannu da wasu kayayyaki.

A ƙaramar hukumar Shinkafi, dakarun tare da haɗin gwiwar Mobile Police Squadron, sun samu sahihan bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’adda a yankin Kwanar Jolof.

A wani sumame da aka gudanar kusa da Maradun, dakarun sun kama wani mutum mai shekaru 35, mai suna Lawali Dan Alo, wanda ake zargi da haɗin gwiwa da ’yan ta’adda da kuma samar musu da kayan more rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *