Hukumar Kashe Gobara ta Birnin Abuja ta ce ma’aikatan kashe gobara uku daga cikin jami’anta sun samu raunuka daban-daban yayin da suke ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi a gidan mai na AYM Shafa, da ke Garki, Abuja, a daren Alhamis.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ibrahim Muhammad, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja.
Muhammad ya ce gidan man da ke Area 3, Garki, ya kama da wuta ne bayan da wata tankar ɗaukar man fetur ta fashe.
A cewarsa, hukumar ta samu rahoton faruwar lamarin da misalin 9:44 na dare, sannan nan take ta tura jami’anta da motocin kashe gobara zuwa wurin.
Muhammad ya ce saboda girman gobarar, sauran hukumomin kashe gobara ma sun shiga aikin ceto, lamarin da ya haifar da haɗin gwiwar hukumomi daban-daban wajen yaƙi da gobarar.
Ya ce a yayin ƙoƙarin shawo kan gobarar da kuma kashe ta, ma’aikatan kashe gobara uku sun samu munanan raunuka.
Ɗaya daga cikinsu a halin yanzu yana karɓar kulawa ta musamman a Cibiyar Kula da Masu Rauni ta Asibitin Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce ƙwararrun likitoci na ƙoƙarin ganin ya farfaɗo, yayin da aka garzaya da sauran ma’aikatan biyu zuwa Asibitin Alliance da ke Area 11, Garki, Abuja, inda suke karɓar magani.
Hukumar ta ce har yanzu ana gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin tashin gobarar.
Muhammad ya buƙaci jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko yin hasashe kan musabbabin gobarar, su jira sakamakon binciken hukuma.
Binciken farko da hukumar ta gudanar dai ya nuna cewa gobarar ta shafi harabar tashar man da kuma wasu gine-ginen da ke kusa da ita bayan da wata tankar mai ɗauke da kusan lita 45,000 na man fetur ta kama da wuta.