Wasu mutanen da ake zargin masu neman tarkacen karafa ne sun lalata ginshiƙan da ke riƙe da gadar da ta haɗa Alakija da FESTAC a Jihar Legas, inda suka fasa simintin ginshiƙan domin cire sandunan ƙarfen da aka saka a ciki.
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar Juma’a, an ga jami’an ‘yan sanda suna kwashe rumfunan da ake zargin masu neman karafa suka kafa a ƙarƙashin gadar.
- Kano – Mutumin da aka kashewa iyalai ya sake angwancewa
- Ƙungiyar tsofaffin sojoji za ta taimaka wajen daƙile yaduwar ƙananan makamai
- Gobara ta tashi a Gidan mai na AY Shafa, a Abuja
Wani mutum da ba a bayyana sunansa ba a cikin bidiyon ya ce an lalata wasu daga cikin ginshiƙan simintin gadar, inda aka cire ƙarfen ƙarfafa ginshiƙan. Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su gaggauta daukar mataki domin hana ci gaba da lalata gadar.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana cewa ta kama wasu mutane 27 da ake zargi da hannu wajen lalata gadar.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce kamen ya biyo bayan gano wani mummunan aikin lalata dukiyar gwamnati a ƙarƙashin gadar.
Wahab ya ce bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun cire sandunan ƙarfe, kayan ƙarafa, igiyoyi da sauran muhimman abubuwa da ke taimakawa wajen tabbatar da ƙarfin gadar.