Wata kotu a Senegal ta yanke wa wasu masu amfani da manhajar TikTok hukuncin daurin gidan yari saboda wasu rubuce-rubuce da suka wallafa, waɗanda ake zargin sun ci mutuncin Shugaban Kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.

Hukuncin ya janyo suka daga wasu masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama, waɗanda suka ce matakin na ƙara nuna damuwar da ake da ita kan ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma ’yancin bayyana ra’ayi a kafafen sada zumunta a Senegal.

Shugaba Faye ya kuma ƙaddamar da tasa jam’iyyar siyasa kwanan nan, lamarin da ya ƙara zurfafa rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin biyu.

Hukuncin ya shafi Mandoumbe Diop, wanda aka fi sani a kafafen sada zumunta da Lamignou Darou.

Kotun ta yanke masa hukuncin watanni uku a gidan yari

Sauran sun haɗa da Magueye Diaw, wanda aka fi sani da Oustaz Thiep, da kuma Moustapha Ndiaye, wanda aka fi sani da Ndiaye Touba, kowannensu an yanke masa hukuncin watanni biyu a gidan yari

An kuma ci tarar kowannensu CFA 500,000, wato kusan dala 800, a cewar lauyansu.

Hukuncin ya zo ne a lokacin da ake fama da rashin tabbas a harkokin siyasar Senegal, biyo bayan rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin Shugaba Bassirou Diomaye Faye da Ousmane Sonko.

A baya, shugabannin biyu sun yi aiki tare, kuma kowannensu ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓakar harkar siyasar PASTEF.

Sai dai rashin jituwarsu a bainar jama’a ya bayyana rarrabuwar kawuna da ke cikin tawagar siyasar da ke mulkin ƙasar.

Lamarin ya kuma sake buɗe muhawara kan iyakar da ya kamata a sanya wa maganganun da ake wallafawa a kafafen sada zumunta, da kuma yadda gwamnati za ta daidaita tsakanin kare mutuncin shugabanni da tabbatar da ’yancin faɗar albarkacin baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *