Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya umarci dukkan hukumomin gwamnati da su daina amfani da kalmomin “watchmen” ko “guards” wajen kiran jami’an tsaro masu zaman kansu, yana mai cewa waɗannan kalmomi na rage daraja da mutuncin wannan sana’a

Da yake jawabi yayin da ya karɓi baƙuncin jami’an tsaro masu zaman kansu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Nairobi ranar Alhamis, Ruto ya ce waɗannan sunaye ragowar tunanin ‘yan mulkin mallaka ne, da ya kamata a maye gurbin su da sunayen da ke nuna girmamawa ga irin gudummawar da jami’an ke bayarwa wajen tabbatar da tsaron ƙasa

Shugaban ƙasar ya amince cewa har yanzu, ana amfani da waɗannan kalmomi a wasu dokoki da ƙa’idojin gwamnati, amma ya ce za a sake duba dokokin domin su dace da matsayin da ake bai wa jami’an tsaro masu zaman kansu a halin yanzu

Ya bayyana cewa za a yi gyare-gyare a dokokin Hukumar Kula da Harkokin Tsaro Masu Zaman Kansu, domin daidaita albashin da ake biyan su da na jami’an tsaro na gwamnati, da sauran ƙa’idoji da zasu nuna muhimmiyar rawar da jami’an tsaron ke takawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *