Ƙungiyar Tsofaffin Sojin Najeriya (REMENAF), reshen Jihar Borno, ta bayyana shirin ta na haɗa kai da Cibiyar Kula da Yaƙi da Ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin Ɗauka ta Ƙasa (NCCSALW), domin yaƙi da ta’addanci da kuma yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Arewa maso Gabas
Shugaban ƙungiyar Laftanar Bukar Kyari Aji (Mai Ritaya), ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da ƙungiyar ta kai wa Cibiyar Kula da Yaƙi da Ƙananan Makamai da ke Maiduguri
- Kawar da haramtattun tashoshin ɗaukar fasinja a Birnin Tarayyar Najeriya
- Gobara ta tashi a Gidan mai na AY Shafa, a Abuja
- ‘Yan sanda sun kama mutum biyar kan raba maganin gargajiya ba tare da izini ba a Kano
Aji ya tabbatar da cewa ƙungiyar tsofaffin Sojin za ta kasance muhimmiyar majiya ta tattarawa tare da raba bayanan sirri ga cibiyar, tare da yin aiki kafada da kafada domin kawar da matsalar yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba a cikin al’umma
Ya kuma bayyana cewa manufar ziyarar ita ce nuna cikakken goyon baya, biyayya da jajircewar tsofaffin sojojin ga Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro wajen yaƙi da ta’addanci a jihar
A nasa jawabin, Manjo Janar Abubakar Adamu (Mai Ritaya), Daraktan Shiyyar Arewa maso Gabas na NCCSALW, ya nuna farin cikin sa tare da bayyana shirinsa na yin aiki tare da tsofaffin sojojin domin yaƙi da matsalar ta’addanci da yaɗuwar ƙananan makamai da makamai masu sauƙin ɗauka
Ya ce wannan haɗin gwiwa yana da matuƙar muhimmanci wajen tattarawa da kawar da ƙananan makamai da makamai masu sauƙin ɗauka a yankin.