Masu zanga-zangar adawa da nadin Farfesa Abdullahi Ahmed, a matsayin Shugaban Kwalejin Tarayya Ta Binciken Lafiyar Dabbobi (FCAHPT) da ke Vom, a karamar hukumar Jos ta kudu, Jihar Filato, sun sake fitowa ranar Jumma’a, inda suka ci gaba da bayyana adawarsu.

Masu zanga-zangar sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya maye gurbin Farfesa Ahmed da Dokta Luka Pam, wanda suka bayyana a matsayin dan asalin yankin kuma kabilar Berom.

Ko a watan da ya gabata sai da masu zanga-zangar suka rufe kofar shiga makarantar, inda hakan ya haifar da tsaiko wajen rantsar da sabon shugaban.

Zanga-zangar ta kuma kawo cikas ga ayyukan ilimi, lamarin da ya tilasata aka dakatar da dalibaidaga rubuta jarrabawa kafin daga bisani wasu shuwagabanni suka shiga tsakani don sasanci.

Da yake magana da manema labarai yayin zanga-zangar wancan lokacin, Shugaban kungiyar (Berom Intelligentsia Forum), Barrista Weng Emmanuel Logyang, ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne domin neman a baiwa al’ummar da ta karɓi bakuncin kwalegin damar jagorantar makarantar.

A cewar Logyang, ‘yan kabilar Berom ba su taɓa riƙe babban matsayi ba a cikin cibiyoyi 4 na tarayya da aka kafa a kan filin da iyayen su suka ba da shi sama da ƙarni ɗaya da ya gabata.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta soke naɗin Farfesa Ahmed, ta naɗa Dr. Pam a maimakon sa.

Sai dai har izuwa hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga wajen gwamnati kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *