Masu zanga-zangar adawa da nadin Shugaban Kwalejin Bincike a Kan Lafiyar Dabbobi ta Tarayya (FCAHPT) sun hana shiga ko fita daga harabar makarantar, lamarin da a ranar farko ya kawo cikas ga jarrabawar dalibai

Wasu masu sharhi a kan al’amuran yau da kulum sun yi gargadin cewa a garin neman gira, mazauna garin Vom na Jihar Filato, yankin da Kwalejin Bincike a Kan Lafiyar Dabbobi ta Tarayya (FCAHPT) take, ka iya rasa ido.

Wannan gargadi dai ya biyo bayan wani jerin manga-zanga da mutanen yankin suka yi don nuna adawa da naɗin Farfesa Abdullahi Ahmed, a matsayin Shugaban Kwalejin.

Ranar Juma’ar da ta gabata masu zanga-zangar suka sake fita suna kira da sai Gwamnatin Tarayya ta janye nadin Farfesan ta kuma maye gurbinsa da Mataimakin Farfesa Luka Pam, wanda suka ce dan asalin yankin ne.

Da yake tsokaci a kan lamarain a wata hira da Blueprint Radio a harshen mako, mawallafin Jaridar The Beacon kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Mista Shabul Mazadu, ya yi kira ga al’ummar Vom da su buji zuwa rafi.

‘Kada fa allura ta tono garma’

“Ina son su san wani abu guda ɗaya: idan aka san su da wannan hali, gobe duk wani abin da Gwamnati za ta yi idan ya shafi jama’a babu wanda zai goyi bayan a kawo abin yankinsu kuma idan aka ci gaba da yin haka, duk wanda aka tura shi aiki yankin zai ji tsoron zuwa; za a iya barinsu su kaɗai da junan su. Kuma idan aka bar su su da junansu garin ba zai taɓa ci gaba a haka ba,” inji Mista Mazadu.

Idan aka san su da wannan hali, gobe duk wani abin da Gwamnati za ta yi idan ya shafi jama’a babu wanda zai goyi bayan a kawo abin yankinsu…

Mawallafin ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su rika sara suna duban bakin gatari don kada allra ta tono garma.

“Idan suka yi wani kuskuren da zai iya janyo tashin hankali, Gwamnati tana da ‘yancin [dauke] makarantar daga yankin baki ɗaya.

“To idan Gwamnati ta [dauke] makarantar baki ɗaya daga yankin, wane ne ke da asara?”

Ya kuma kara da cewa da za a yi waiwaye za a ga ko birnin Jos ma ba ‘yan asalin yankin kadar ne suka gina shi ba.

“Gina Jos ma ba ‘yan garin ne suka yi ba, wadansu daga wasu wurare ne suka zo, suka zuba hannun jari suka zauna kuma gwamnati ma tana samun kuɗaɗen shiga daga wajen su,” inji shi.

‘Ba wannan ba ne karo na farko’

Shi kuwa Kwamared Muhammad Tanko Shitu, wakilin Jaridar Blueprint a Jos kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, cewa ya yi wannan matsala al’ummar Jihar Filato gaba daya za ta safa ba garin Vom ko Karamar Hukumar Jos ta Kudu kadai ba.

“’Ya’yan Jihar Filato suna zuwa wasu wurare suna riƙe madafun iko a hukumomin Gwamnatin Tarayya da sauransu, babu wanda yake nuna mana tsangwama irin wannan – saboda haka ba mu ga dalilin da zai sa idan ‘ya’yan wasu wurare suka zo mana irin wannan abubuwan suke rika faruwa ba,” inji shi.

A cewar Kwamared Shitu, ba wannan ne karo na farko ba a yankin na Vom da ma Jihar Filato da ake tayar da jijyoyin wuya saboda wani nadi da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Kusan shekara ashirin da suka wuce, inji Kwamared, a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, an yi wa marigayi Dokta Abubakar Lamurde, tsohon Shugaban Cibiyar Bincike  a Kan Magunguna Dabbobi ta Ƙasa (NVRI) a garin na Vom zanga-zangar adawa da naɗinsa.

Ya ƙara da cewa, an sake gudanar da irin wannan zanga-zangar adawar yayin da aka naɗa marigayi Alhaji Mukhtar Mohammed a matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi da Talauci ta Kasa (NAPEP), lokacin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.

“Akwai marigayi Dokta Abubakar Lamurde, shi ne Shugaba a cibiyar NVRI, Vom – waɗannan mutane sun yi ta yin zanga-zanga a wancan lokacin har ta kai ga da ƙarfin tsiya suka shiga suka fito da shi daga cikin ofishinsa suka ce ba su aminta da ya jagoranci wannan cibiyar ba.

“Haka Gwamnatin Tarayya a ƙarkashin [Cif Olusegun] Obasanjo a wancan lokacin ta biye musu – aka yi wa mutumin nan wulaƙanci kuma Gwmnati ta cire shi aka maye gurbinsa da wata Dokta Lami wadda ta zama Farfesa daga baya,” indi Kwamared Shitu.

Dokta Abubakar Lamurde, shi ne Shugaba a cibiyar NVRI, Vom – waɗannan mutane sun yi ta yin zanga-zanga a wancan lokacin har ta kai ga da ƙarfin tsiya suka shiga suka fito da shi daga cikin ofishinsa suka ce ba su aminta da ya jagoranci wannan cibiyar ba.

Mataki na gaba

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani martani daga Gwamnatin Tarayya a kan matakin da za ta dauka.

Wasu manazarta suna ganin yin abin da masu zanga-zangar suje so zai kara musu kwarin gwiwa su ci gaba da yin haka, sannan kuma ya sa al’ummomi a wasu sassan kasar na ma za su rika tayar da kayar baya idan aka nadi wanda ba dan kabilarsu ko dan yanking ba ya shugabancin wata hukuma ta tarayya.

A ganin Mista Shabul Mazadu bai kamata Gwamnati ta biye wa masu zanga-zangar ba sai idan yin hakan ya zama dole.

“Ba na goyon bayan gwamnati ta janye naɗin, amma idan ta ga abin ya ƙi ƙarewa kuma zai haifar da a lalata makarantar ko zai iya zama barazana ga rayuwar mutumin, to sai ta zauna ta duba da kyau; amma ya kamata Gwamnatin Jiha da ta Tarayya su yi magana a kan wannan abin, a wayar da kan al’umma”.

Shi kuwa Kwamared Muhammad Tanko Shitu cewa ya yi dabara ta rage ga mai shiga rijiya – ma’ana Gwamnati ka iya daukar matakin janye nadin ko ta yi mursisi – amma ko ma me ta yi, to akwai sharadi.

“Idan Gwamnati ta bar shi, to, ta ba shi tsaro mai inganci domin ya samu nutsuwa ya kwantar da hankali ya bai wa ƙasa gudumuwarsa domin samun ci gaba.

“Idan kuma Gwamnati ta [sauya] shi, ta biye musu, an tabbatar da wani abu wanda ba zai kawo ci gaban ƙasa da ci gaban wannan cibiyar da kuma zaman lafiya a cikin Najeriya ba,” inji Kwamared Shitu.

Korafin masu zanga-zangar

Don ganin damarın bai rikide ya zama wani abu na daban ba, Mista Shabul Mazadu ya yi kira ga Gwamnati a dukkan matakai da ta wayar da kan al’umma a kan yadda tsarin naɗin jagororin ma’aikatun Gwamnatin Tarayya yake.

“Zai iya yiwuwa wannan zanga-zangar da ake yi akwai waɗanɗa suke zuga mutane su ga kamar ana danne mutanensu ne, suna ganin an yi abu a garinsu kuma dole ne a bai wa ɗan garin shugabanci.

“Amma ba haka ya kamata ya kasance ba; abinda ya shafi Gwmnatin Tarayya ba abin da za a mayar da shi kamar na ƙabilanci ko na Jiha ba ne,” in ji Mazadu.

Sai dai masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa tun kafin samun mulkin Najeriya al’ummar yankin ta bayar da matsuguna ga Cibiyar NVRI da sauran cibiyoyin da suke karkashinta, amma har yanzu ba su ci moriyar wannan sadaukarwa ta fuskar shugabanci ba.

Sun kuma yi ikirarin cewa Mataimakin Farfesa Pam yana cikin mutanepn da suka nemi shugabancin Kwalejin ta FCAHPT amma aka nuna mishi wariya.

Da yake magana da manema labarai yayin gudanar da zanga-zangarsu ta farko a watan Yuli, Shugaban Kungiyar ‘Yan Bokon Kabilar Berom, Barrista Weng Emmanuel Logyang, ya ce suna neman a bai wa al’ummar da ta karɓi bakuncin Kwalejin damar jagorantar makarantar.

A cewar Logyang, ‘yan kabilar Berom ba su taɓa riƙe babban matsayi ba a cibiyoyi hudu na tarayya da aka kafa a filin da iyayensu suka bayar shi sama da ƙarni ɗaya da ya gabata.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta soke naɗin Farfesa Ahmed, ta naɗa Mataimakin Farfesa Pam a madadinsa.

Wannan takaddama ta jawo muhawara a fadin Najeriya game da şahincin wadannan bukatu yayin da ‘yan kasa suda zuba İdo su ga wanne mataki Gwamnati za ta dauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *