Hukumar Wasanni ta Kasa (NSC) ta sanar da sabon ƙunshin ladan kuɗi don ƙarfafa gwiwar tawagar Super Falcons ta Najeriya, bayan da kungiyar ta samu tikitin buga wasan kwata-fainal na Gasar Cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON) ta 2026.

Shugaban Hukumar (NSC), Shehu Dikko, ya bayyana cewa hukumar ta ninka ladan duk ƙwallon da aka ci daga dala 5,000 zuwa dala 10,000 saboda kyawawan wasanni da tawagar ta buga a matakin rukuni.

Bugu da ƙari, NSC ta ce an samu ƙarin wani tallafi daga wasu bangarori, wanda Shugaban Hukumar Kwastam na Najeriya ya sanar, inda su kayi alƙawarin bayar da dala 10,000 ga kowace ƙwallo da ‘yan wasan na Super Falcons za su ci a tsawon gasar.

Idan aka haɗa da ƙwallaye 6 da tawagar ta ci a wasan da ta doke ƙasar Masar a matakin rukuni, jimillar ladan kuɗaɗen da za su samu daga Hukumar (NSC) da kuma wasu bangarori ya kai dala 120,000.

Har ila yau, NSC ta bayar da umarni ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) da ta biya Super Falcons cikakken kuɗin alawus na duk wasanni 3 da suka buga na rukuni, ciki har da wanda ta yi rashin nasara a hannun Malawi.

Najeriya ta tabbatar da zuwa kwata-fainal bayan ta lashe wasanni 2 cikin 3 na rukuni, inda ta ƙare a matsayi na biyu a rukunin D da maki 6, wanda take shirin karawa da ‘yan wasan Kamaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *