Mai rike da kofin Gasar Kwararrun Kwallon Kafa ta Najeriya (NPFL) Rangers International FC, ta zama zakaran Gasar Super 6 ta 2026 bayan lallasa mai masaukin baki, Plateau United da ci 1-0 a wasan karshe da suka buga a sabon filin wasa na garin Jos, a ranar Lahadi.
Kwallar da Justice Akugre ya ci da kai a minti na 28 ita ce ta bai wa zakaran NPFL ta bara nasarar doke Plateau United wadda ake yiwa lakabi da “Peace Boys.”
Mai masaukin bakin ta yi kokarin farke Kwallon da aka zura mata a raga, inda ta matsa lamba sosai amma ‘yan wasan Rangers sun yi tsayuwar mai daka wajen kare hare-haren da aka kai musu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
- Newcastle da Liverpool sun tashi kunnen doki 2–2 a St James’ Park
- Man City ta cimma yarjejeniya da Lille don sayan dan wasan Marokko Ayyoub Bouaddi
- Brighton ta ragargaji Aston Villa, Manchester City ta sha da kyar a hannun Bournemouth
A wani labari na daban, kungiyar Mighty Jets na garin Jos, ta zo na uku a Gasar NPFL Super 6 bayan doke kungiyar Katsina United da ci 1-0 a wasan da suka buga a sabon filin wasa na garin Jos, a ranar Lahadi.
Dan wasa Tochukwu Ibedu, shi ya ci wata kwallo mai ban sha’awa a minti na 39 wadda ta baiwa Mighty Jets nasara yayin fafatawar.
Kungiyoyi shida ne wadanda suka hada da Rangers International FC, da Rivers United, da Plateau United, da El-Kanemi Warriors, da Mighty Jets da kuma Katsina United suka fafata a Gasar ta NPFL Super 6 ta 2026.
A na shirya Gasar Super 6 ne domin kungiyoyin da ke buga Gasar NPFL da suka samu gurbin fafata Gasar Zakarun Nahiyar Afirka da kuma Confederation Cup su fara shiri mai kyau da wuri domin samun nasara.