Wata haɗaɗatacciyar tawagar jami’an kashe gobara ta tarayya da ta jihar Kwara a ranar Lahadi ta fafata da wata babbar gobara da ta shafi wani babban gini mai hawa ɗaya, wanda ya ƙunshi gidaje masu ɗakuna uku-uku guda biyu da kuma shaguna guda 10.

Wakilin Blueprint.ng ya kalto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:36 na rana a Ita-Amodu, daidai mahaɗar Niger Junction da ke Ilorin, cikin ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a babban birnin jihar.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce hukumar kashe gobara ta jihar ta tura motocin kashe gobara guda biyu zuwa wurin da lamarin ya faru saboda girman gobarar.

Kakakin ya ce har yanzu ana binciken musabbabin gobarar, kuma za a bayyana ƙarin sakamako idan an kammala binciken.

“Daga cikin kayayyakin da gobarar ta shafa har da katifu da kujerun sofa masu saurin kama wuta, saboda kayan da aka yi amfani da su wajen kera su, wanda hakan ya taimaka wa tsanani da kuma saurin yaɗuwar gobarar.

“Lokacin da muka isa, motar kashe gobara ta farko ta tarar gobarar ta riga ta yi ƙarfi sosai kuma ta mamaye ginin.

Saboda girman gobarar, nan da nan aka tura motar kashe gobara ta biyu domin ƙarfafa aikin kashe gobarar,” in ji shi.

Adekunle ya yaba da jarumta, ƙwarewa, da kuma juriya da jami’an kashe gobarar suka nuna, wanda ya ce hakan ya hana gobarar yaɗuwa zuwa wasu gine-ginen da ke maƙwabtaka da su.

“Ƙoƙarin haɗin gwiwa da suka yi ya yi nasarar shawo kan gobarar da misalin ƙarfe 14:05 na rana,” in ji shi.

Ya ce haɗin gwiwar da aka yi tsakanin hukumomin kashe gobara na tarayya da na jihar ya taimaka sosai wajen rage tasirin gobarar da kuma hana ta ƙara ruruwa.

Babban jami’an hukumar kashe gobara na jihar, Alabi Muhammed, ya yaba da hazaka, juriya, da kuma kyakkyawan aikin haɗin gwiwa da mutane da jami’an hukumomin kashe gobara biyu suka nuna wajen shawo kan gobarar da ke cin kishirwa.

Ya buƙaci masu mallakar kasuwanci da masu gudanar da sana’o’in da ke hulɗa da kayayyaki masu saurin kama wuta kamar katifu, kujeru, da sauran kayayyaki makamantansu da su ba da fifiko ga matakan tsaro na gobarar, su kiyaye tazara mai kyau tsakanin kayayyaki masu saurin kama wuta, kuma su samar da ingantattun kayan kashe gobara a cikin wuraren kasuwancinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *