Omar Marmoush ya zura ƙwallaye biyu cikin mintuna uku a rabin wasa na biyu, yayin da Manchester City ta farfaɗo daga baya ta doke Atletico Madrid a wasan sada zumunta da suka buga a Seoul, dake ƙasar Koriya ta Kudu.
Ƙungiyar ƙasar Spaniya ce ta fara zura ƙwallo kafin ƙarshen rabin farko. Bayan City ta kasa fitar da ƙwallon da Koke ya buga na kusurwa, Morten Hjulmand ya ba Jorge Dominguez dan shekara 16 damar bugawa, wanda ya buga ƙwallo ta wuce mai tsaron ragar City, Gianluigi Donnarumma.
Amma City ta farke ƙwallon a minti na 57. Antoine Semenyo ya nuna ƙwazo yayin da ya zame amma bai bar ƙwallon ya fita daga cikin filin wasa ba, sannan ya kutsa daga gefen hagu ya mika wa Marmoush wadda ya jefa ta cikin raga.

-
WAFU B U20: Flying Eagles na fatan rama abinda Burkina Faso ta yi mata —- Maikaba
-
WAFCON: Marokko ta doke Afirka ta Kudu 2-1
-
Super Falcons ta samu ƙarin ƙuɗaɗen alawus
Sun sake maimaita irin hakan bayan mintuna 2 da cin wata ƙwallo mai kama da irin wannan, inda Marmoush ya sake nuna kwazo bayan Semenyo ya sake miƙa masa ƙwallo daga ɓangaren hagu.
Mutane sama da 50,000 ne suka kalli wasan a Filin wasa na Seoul World Cup stadiya.
Rayan Ait-Nouri ne ya ƙara ƙwallo ta 3 a ƙarin lokaci
Wannan shi ne wasa na uku kuma na ƙarshe da City za ta buga a yankin Asiya, yayin da take shirye-shiryen fara sabon kaka.
City ta sha kashi a bugun fenareti da ci 3-1 a hannun Inter Milan bayan sun tashi 1-1 a Hong Kong a ranar 1 ga Agusta, sannan kuma sun doke tawagar K League All-Stars da ci 3-1 a Seoul ranar Laraba.
City, wadda ta doke Chelsea 1-0 a wasan ƙarshe na FA Cup a watan Mayu, wasansu na gaba zai kasance ne ranar Lahadi, 16 ga Agusta, inda za su buga da zakaran Gasar Firimiyar Ingila, wato, Arsenal, a wasan Community Shield a Filin Principality Stadiya da ke Cardiff.
