Kimanin mutane goma sha shida ne suka samu raunika bayan da wani gini ya rufta a anguwar Ɗandinshe, kwanar Yashi dake ƙaramar hukumar Fagge ta Jihar Kano.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 4:32 na asuba daga ɗaya daga cikin ma’aikatanta, Aminu Sani Warure.

Abdullahi ya ce jami’an hukumar sun gaggauta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da wani gini mai faɗin ƙafa 20×30 ya rufta tare da danne mazauna cikin sa.

Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai Al-Mustapha Yusuf, mai shekaru 15; Khadija Yusuf, mai shekaru 7; Ummusalama Yusuf, mai shekaru 10; Madina Yusuf, mai shekaru 6; Hafsat Yusuf, mai shekaru 9, da wasu mutum takwas waɗanda ba a samu sunayensu nan take ba.

Sai dai Abdullahi yace jami’an hukumar sunyi nasarar ceto wasu mutane Uku da ransu a cikin ɓaraguzan ginin.

Abdullahi ya ce har  yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin.

Ya shawarci mazauna yankin da su ƙara taka-tsantsan a lokacin damina domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *