Iran ta gindaya wasu sharuɗɗa kafin ta sake buɗe mashigar Hormuz, ciki har da biyan diyya kan asarar da yaƙin mata, da kuma ɗage takunkuman da aka kakaba mata.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce tattaunawar da suke yi da Oman kan zirga-zirga da kuma yadda za a gudanar da mashigar na dab da kammala, amma ya jaddada cewa sake buɗe mashigar zai dogara ne da cika sharuɗɗan.
Ya ce Iran na neman a biya ta diyya kan abin da ta bayyana a matsayin keta yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuni.
- Yara sama da 300 sun mutu sakamakon Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo
- Senegal — kotu ta ɗaure ‘yan tiktok kan zargin sukar shugaba Faye
- Dumamar yanayi na barazana ga yara fiye da biliyan 1 – UNICEF
An jiyo Shugaban rundunar tsaron ƙasar Mohammad Bagher Zolghadr na bayyana wasu buƙatu da Iran ta gindaya kafin sake buɗe mashigar, ciki har da kawo ƙarshen abin da ya kira hare-haren wuce gona da iri kan Iran da ƙawayenta a Lebanon, Falasɗinu, Yemen da Iraki.
Ya kuma nemi a ɗage wani shingen ruwa na sojojin ruwan Amurka, cire takunkuman da aka kakaba mata, sannan a saki kadarorin da ta mallaka a ƙetare, kuma a biya ta diyyar asarar da yaƙin ya haddasa mata.
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta ce batun sake buɗe mashigar ya bambanta da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Oman, tana mai dagewa cewa duk wata yarjejeniya dole ne ta amince da sharuɗɗan Tehran.
Wannan na faruwa ne yayin da zirga-zirgar jiragen ruwa ta ragu a mashigar ruwan, inda ake zargin Iran da kai wa wasu jiragen ruwa hari bisa zargin kauce wa hanyar da ta kamata su bi.
Mashigar Hormuz, wadda na daga cikin manyan hanyoyin jigilar makamashi a duniya, na ci gaba da zama babban abin damuwa ga ƙasashen duniya saboda muhimmancin da take dashi wajen jigilar mai da iskar gas a duniya.