Super Falcons ta Najeriya ta kasa samun tikiti kai tsaye na shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027 wanda za ayi a Brazil, bayan Kamaru ta doke ta da ci 1-0 a wasan kwata-fainal na Gasar WAFCON ta 2026 da suka buga a ranar Lahadi.

An buga wasan ne a filin wasa na Larbi Zaouli da ke Casablanca, a Marokko. Kwallon da Nyadjou ta zura a minti na 19 shi ya baiwa Kamaru nasara kuma ya rushe burin Super Falcons na samun damar zuwa Brazil kai tsaye.

Duk da yunkurin da suka yi a rabi na biyu karkashin jagorancin gogaggiyar ‘yar wasa Asisat Oshoala da kyaftin Rasheedat Ajibade, Najeriya ba ta iya keta ‘yan wasan bayan Kamaru masu karfi ba.

Wannan shan kaye ya zama tarihi ga zakarun Super Falcons wadda ta lashe kofin Afirka sau 10, kuma suka shigo gasar a matsayin masu rike da kofin.

Tun da farko dai a gasar, tawagar Koci Justin Madugu ta fara da shan kashi mai ban mamaki da ci 3-2 a hannun Malawi wadda ta fara halartar gasar a wannan karo a tarihi. Ko da yake daga baya Super Falcons ta dawo da kokarin ta inda ta samu nasarar doke Zambia da ci 1-0, da kuma murkushe Masar da ci 6-2.

Duk da cewa Najeriya ta rasa cancantar shiga Gasar cin Kofin Duniya ta Mata kai tsaye da aka baiwa wadanda suka kai wasan kusa da na karshe na WAFCON burin su na shiga Gasar Duniya bai kare ba tukuna. Super Falcons yanzu za ta jira wasannin Playoff da za a fara bugawa ranar 13 ga Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *