Masu amfani da sadarwa a Najeriya sun yi amfani da data mai girman Terabyte miliyan 1 da rabi a watan Mayu, wanda shi ne mafi girman yawan amfani da aka taɓa samu a cikin wata ɗaya.

Haka Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayyana a sabon bayanan da ta fitar.

A cewar Hukumar NCC, ƙaruwar amfani da data a Najeriya ya samo asali ne daga yadda mutane da dama ke sauyawa zuwa sabbin hanyoyin sadarwa na 4G da 5G, wanda ke ba da sauri mafi girma.

Har ila yau, ƙaruwar masu amfani da fasahar zamani ya ƙara taka muhimmiyar rawa wajen amfani da data a ƙasar, kamar yadda Hukumar NCC ta bayyana.

A farkon wannan shekarar, Shugaban Hukumar NCC, Dr. Aminu Maida, ya ce ‘yan Najeriya na cinye kimanin Terabyte 45,800 na data a kowace rana. Hakan ya nuna yadda ƙasar ke ƙara dogaro da ayyukan intanet da shafukan sada zumunta.

Maida ya ce ƙaruwar amfani da data ta samo asali ne biyo bayan bunƙasar tattalin arziki na zamani a Najeriya. Wannan ya haɗa da biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani, da shafukan saye da siyarwa ta yanar gizo da sauran su.

Masana a fannin sadarwa sun ce babban abin da ya sa aka ƙara amfani da data shi ne buƙatar ‘yan Najeriya na samun kuɗi ta intanet, musamman ta kafafe irin su Facebook, da TikTok, da YouTube, da kuma X.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *