Sanata mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, ya bar hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun da ke Osogbo, bayan shafe sa’o’i yana amsa tambayoyi kan kalaman da ake zargin ya yin yakin neman zabe.

Fadahunsi ya je sashen binciken manyan laifuka na rundunar yan sanda a ranar Laraba, domin amsa gayyatar ’yan sanda kan wani bidiyon yakin neman zaben jam’iyyar APC da aka dauka a Ilesa.

A cikin bidiyon, an fassara kalaman sanatan a matsayin kira ga magoya bayansa da su “kashe” wasu mambobin jam’iyyar Accord, wadda ke hamayya da APC a zaben gwamnan jihar.

A ranar Talata ne Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun ta umurci Fadahunsi da ya bayyana a gaban SCID, tana mai cewa kalaman da ake danganta masa na iya zama barazana da tayar da zaune tsaye, tare da kara dagula yanayin siyasa gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.

Bayan shafe sa’o’i a hedikwatar ’yan sandan, an ga Fadahunsi yana fita daga wurin tare da tawagarsa a wani bidiyo da News Central ta wallafa.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san cikakken abin da aka tattauna yayin binciken ba, yayin da rundunar ’yan sandan da sanatan ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Zaben gwamnan jihar Osun zai gudana ranar Asabar, inda gwamna mai ci, Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP, ke neman wa’adin mulki na biyu.

Adeleke zai fafata da ’yan takarar APC, Accord da sauran jam’iyyun siyasa.

Yayin da zaben ke kara gabatowa, an samu karuwar tashe-tashen hankula na siyasa a jihar, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka kara sanya ido a fadin Osun.

Fadahunsi na wakiltar mazabar Osun ta Gabas a Majalisar Dattawa, kuma yana daga cikin fitattun ’yan siyasar adawa a jihar. Ya kuma kasance cikin masu taka rawa a yakin neman zaben APC na kujerar gwamnan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *