Desire Doue ya nuna jarumta inda ya ci kwallo ɗaya da kuma bayar da taimakako aka ci wata, yayin da Paris Saint-Germain ta doke Aston Villa da ci 2-1 don lashe kofin Super Cup.

PSG, mai rike da kofin Zakarun Turai ta fuskanci daga wajen Aston Villa, wadda ta lashe Gasar Europa League na bara, domin ɗan wasan gaba mai shekaru 17, Brian Madjo, ya addabi PSG a duk tsawon wasan da aka buga a ranar Laraba a Salzburg.

Doue ne ya baiwa Khvicha Kvaratskhelia taimakon ƙwallon farko mai kyau da ya ci, amma Madjo, wanda Villa ta sayo daga Metz a watan Janairu, ya zubar da dama da yawa kafin daga baya ya farke ƙwallon da aka ci su a ƙarshen rabi na farko.

Kwallon da Doue ya ci cikin kwanciyar hankali a minti na 61 ita ta tabbatar da cewa PSG ta zama ƙungiya ta huɗu da ta kare kofin Super Cup, kuma ta farko tun bayan Real Madrid a 2017.

Haka kuma Luis Enrique ya zama koci na uku kawai da ya lashe Super Cup sau 3. Ya taɓa lashe wa da Barcelona a 2015 a kan Sevilla, da kuma PSG, bara a kan Tottenham. Carlo Ancelotti ya lashe sau 5 da Pep Guardiola sau 4, su ne suka fi shi lashe wannan kofin.

PSG ta kuma shiga jerin ƙungiyoyin da suka lashe wannan kofi shekaru 2 a jere, tare da Ajax 1973, 1974, AC Milan 1989, 1990 da Real Madrid 2016, 2017.

A gefe guda, Doue ya zama ɗan wasa na farko da ya ci kwallo kuma ya bayar da taimako aka ci wata kwallo a wasa ɗaya na Super Cup tun 2015, lokacin da Luis Suarez ya yi haka ga Barcelona na Luis Enrique, a kan Sevilla ta Unai Emery.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *