Kamaru ta tsallaka zuwa wasan ƙarshe na Gasar cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON) ta 2026, a daren Laraba bayan ta doke mai masaukin baƙi, Marokko da ci 3-1 a bugun fenariti, bayan wasan ya ƙare a cikin fili babu ci a Rabat.

Kamaru ta ci kwallaye 3 a bugun fenariti 4 da ta buga ta hannun Marie Ngah, da Rose Bella da kuma Myriam Nyadjou, yayin da Marokko ta iya cin ɗaya kawai ta hannun Hanane Aït El Haj.

Kenza Chapelle, da Meryem Atiq da kuma Sakina Ouzraoui duk sun kasa cin nasu bugun fenariti ga Atlas Lionesses.

Kamaru ta kara cimma wannan babban nasarar ne bayan ta kawar da zakaran gasar wato, Najeriya da ci 1-0 a wasan kwata-fainal.

Mai tsaron ragar Kamaru, Bihina Michaely, ta lashe kyautar ‘yar wasan da ta fi bajinta bayan ta daƙile bugun fenariti 4 yayin karawar; daya a cikin fili, uku kuma lokacin bukun fenariti.

Wannan nasara ta kai Kamaru zuwa wasan ƙarshe na WAFCON a karo na huɗu, kuma ta kawo ƙarshen begen da Marokko ke yi na buga wasan ƙarshe na nahiyar a karo na uku a jere.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *