Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce ta fara sake buga takardun zaɓen gwamnan Jihar Osun domin saka sunan ɗan takarar jam’iyyar SDP, Dr Francis Olugbenga Ajala, da abokin takararsa Faseke Babajimi Oladipo.

INEC ta ce matakin ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na ranar 22 ga Yuli, 2026, wanda ya umarci hukumar da ta amince da Ajala a matsayin ɗan takarar SDP tare da sanya sunansa da bayanansa cikin takardun zaɓen.

Hukumar ta ce sabbin takardun zaɓen za su isa Jihar Osun a ranar Alhamis, 13 ga Agusta, sannan a rarraba su zuwa ofisoshin ƙananan hukumomi a jihar kafin zaɓen ranar Asabar.

Da shigar SDP cikin zaɓen, adadin jam’iyyun da za su fafata a zaɓen gwamnan Osun ya koma 15.

INEC ta ce an kuma sake buga takardun tattara sakamako domin su dace da sabon tsarin zaɓen.

A wani mataki na ƙara bai wa ma’aikata damar shiga zaɓen, Gwamna Ademola Adeleke ya ayyana Juma’a, 14 ga Agusta a matsayin ranar hutu daga aiki ga ma’aikatan gwamnati a jihar, domin su samu damar yin tafiye-tafiye zuwa wuraren da za su kaɗa ƙuri’a tare da shirye-shiryen zaɓen.

Sai dai waɗanda ke gudanar da ayyukan gaggawa da muhimman ayyuka ba su cikin hutun.

A ɓangaren tsaro kuma, Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Disu, ya tura Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda, DIG Ishyaku Mohammed, zuwa Osun domin jagorantar daidaita ayyukan tsaro a lokacin zaɓen.

’Yan sanda sun ce DIG Mohammed zai yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kare masu zaɓe, jami’an INEC, kayan zaɓe, rumfunan zaɓe, cibiyoyin tattara sakamako da ’yan jarida.

IGP ya kuma gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu kan satar akwatin zaɓe, tsoratar da masu zaɓe, ta’addancin ’yan daba da sauran laifukan zaɓe, yana mai cewa za a kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu.

A gefe guda, wani jigo a APC, Olatunbosun Oyintiloye, ya yi kira ga ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Osun da su guji tashin hankali tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana.

Haka kuma, tsohon ɗan takarar neman kujerar gwamnan Osun a PDP, Adebayo Adedamola, wanda aka fi sani da Fryo, ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen ranar Asabar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *