Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Muhammad Idris, ya bayyana cewa, ba za a iya magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta ta hanyar amfani da ƙarfin soja kaɗai ba.

Ya ce, ana buƙatar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji  da hukumomin tsaro da gwamnatoci a dukkan matakai da al’ummomi da kafafen yaɗa labarai da kuma sauran jama’a.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Cikin Gida, Manjo-Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), ya kai masa ziyarar girmamawa a ma’aikatar dake Abuja.

Ministan ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin tarayya na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da hukumomin zartarwa da al’ummomi da ’yan ƙasa, domin inganta zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasa.

Idris ya yi maraba da ziyarar, yana mai bayyana ta a matsayin wata muhimmiyar dama ta ƙara fahimtar ayyukan sabon Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Cikin Gida, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen sanar da ’yan Najeriya manufofi da shirye-shiryen gwamnati kan tsaro.

Ministan ya ce: “Zaman lafiya da tsaro su ne muhimman ginshiƙai; a gaskiya, su ne tubalan duk wani ci gaba da zai samu a ko’ina.”

Haka kuma, ya bayyana labaran ƙarya da yaɗa bayanan da ba su dace ba, da kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan a matsayin sabbin ƙalubalen tsaron ƙasa.

Ya nanata buƙatar yin amfani da hanyoyin sadarwa cikin gaskiya, tare da ƙara wayar da kan jama’a game da tantance sahihancin bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *