Musulmi da mabiya addinin Kirista sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da nufin ƙarfafa fahimtar juna, mutunta addinan juna da kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu a Najeriya.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a wani babban taron ƙasa da ƙasa da Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (RABITA/MWL) ta gudanar tare da haɗin gwiwar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) a Abuja.
Shugabannin Musulmi da wakilan Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar, wadda ta mayar da hankali kan samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci.
- ‘Yan takarar dake kan gaba a zaben gwamnan jihar Osun
- Najeriya ta jaddada buƙatar ƙara zuba jari a matatun mai na Yammacin Afirika
- ’Yan sanda sun kama shugabannin ASUU na Jami’ar Imo kan yajin aiki
A cewar bayanan da Shafin facebook na JIBWIS Nigeria ya ruwaito, yarjejeniyar ba tana nufin Musulmi da Kiristoci su koma addini ɗaya ba, sai dai tana ƙarfafa kusantar juna, fahimtar koyarwar addinin juna da kuma girmama bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
A yayin taron, jagororin addinan biyu sun gabatar da hujjoji daga Alƙur’ani da kuma Littafi Mai Tsarki da suka yi nuni da muhimmancin zaman lafiya, kyautata mu’amala da girmama juna.
An kuma yanke wasu shawarwari da za a miƙa wa gwamnati domin a duba hanyoyin da za a ƙarfafa su, musamman wajen magance wasu al’adu da matsalolin zamantakewa da kan haifar da rashin jituwa tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Taron ya jaddada cewa ba alheri ba ne Musulmi ya tsangwami Kirista, ko Kirista ya tsangwami Musulmi, musamman kasancewar dukkansu ’yan ƙasa ɗaya ne kuma suna rayuwa tare a cikin al’umma ɗaya.
Masu shirya taron sun bayyana cewa haɗin kai da fahimtar juna da mutunta addini da ’yancin kowane ɗan Adam na daga cikin muhimman hanyoyin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.