Jami’an ’yan sanda a Jihar Imo sun kama shugaban reshen Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, na Jami’ar Jihar Imo (IMSU), Stephen Oguji, da wasu jami’an ƙungiyar, bayan ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani.
Wata majiya daga jami’ar ta ce an kama jami’an ne bayan sun kammala shirin rediyon da suka halarta da safe, inda daga baya aka samu labarin cewa an sake su, bayan shafe wasu sa’o’i ana yi musu tambayoyi.
A ranar Litinin ne ASUU-IMSU ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani, tana mai zargin rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan walwalar malaman jami’o’i da sauran sharuɗɗan aiki a jami’o’in gwamnati.
- Wane ne sabon shugaban hukumar tsaron Iran Mohsen Rezaei
- Iran ta gindaya sharuɗɗan buɗe Mashigar Hormuz
- Nijar – Sojoji 17 sun mutu a haɗarin mota.
Yajin aikin ya zo ne a daidai lokacin da Jami’ar Jihar Imo ke shirin fara jarabawa, lamarin da ya jefa ɗalibai cikin fargaba tare da haifar da damuwa kan yiwuwar katse jadawalin karatun jami’ar.
Ƙungiyar ta ce yarjejeniyar da aka cimma da Gwamnatin Tarayya ta shafi jami’o’in jihohi ma.
Ya zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Imo, DSP Henry Okoye, bai mayar da martani kan tambayoyin da aka aika masa game da kamen jami’an ba.