An naɗa Mohsen Rezaei, tsohon babban kwamandan rundunar Sojojin Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), a matsayin shugaban babbar hukumar tsaron Iran, wadda ke da muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tsaro da harkokin waje na kasar.
Rezaei ya karbi ragamar mukamin sakatararen Majalisar Koli ta Tsaron ƙasa ta Iran (Supreme National Security Council) a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan sake buɗe Mashigar Hormuz, wadda Tehran ke amfani da ita a matsayin wata hanya ta matsin lamba yayin rikicin da ya shafe watanni tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila.
Ya maye gurbin Mohammad Bagher Zolghadr, wanda aka naɗa mai ba da shawara kan siyasa ga Jagoran Koli na Iran, Mojtaba Khamenei.
Kafin Zolghadr, Ali Larijani ne ya riƙe wannan muƙamin, wanda aka kashe a wani hari da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Maris.
- Iran ta gindaya sharuɗɗan buɗe Mashigar Hormuz
- Mayaƙan Houthi sun kai hari matatar man Saudiyya
- Nijar – Sojoji 17 sun mutu a haɗarin mota
Rezaei, mai shekaru 71, ya jagoranci rundunar IRGC daga shekarar 1981 zuwa 1997. Wannan lokaci ya kunshi yakin Iran da Iraki a shekarun 1980, wanda Iran ke kira da (Sacred Defence).
Bayan ya bar shugabancin IRGC, Rezaei ya zama mamba a Majalisar Shura da daidaito ta Iran, wadda ke nazartar dokoki da yadda ya kamata a aiwatar dasu.
Rezaei ya dade yana nuna muhimmancin da Iran ke bai wa ci gaba da rike iko kan Mashigar Hormuz, hanyar ruwa da kusan kashi daya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta cikinta.