Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ya kamata a yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir uzuri kan matsayinsa mai tsauri a harkokin siyasa, yana mai cewa malamin na fuskantar matsanancin nuna wariya ga Musulunci a jihar da yake.
Gumi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce Sheikh Jingir yana cikin tsakiyar guguwar tsananin nuna ƙiyayya da wariya ga Musulunci.
Hakan dai ya biyo bayan wani batu da sheik Jingir yayi a yayin da yake jawabi a wurin bikin auran gata da gwamntin jihar kano ta shirya.
- Rundunar Sojin Najeriya takai hari kan ’Yan Bindiga Da Ke hanyar Shiga Kebbi Daga Zamfara
- Ruftawar gini ta jikkata Mutane 16 a kano
- Zamfara: Soji sun lalata abin fashewa, sun kama mutane biyu
A yayin taron, Sheikh Jingir ya ce ɗan takarar da yake goyon baya shi ne Bola Ahmed Tinubu, saboda ya zabi Musulmi a matsayin mataimakinsa.
A cewarsa, yana daga cikin waɗanda suka yi kira ga jama’a da su goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023, yana mai tambayar, ko laifi ne ya goyi bayan irin wannan tikiti a matsayinsa na Musulmi mai wa’azin addinin Islama.
Sai dai kalaman nasa sun jawo suka daga wasu ’yan Najeriya, waɗanda suka bayyana su a matsayin yin amfani da matsayinsa na malamin addini wajen tallata wani ɗan takarar siyasa, abin da suka ce zai iya cutar da martabar Musulunci a ƙasar.