Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta tura jami’ai 10,210, zuwa Jihar Osun domin taimakawa harkar tsaro gabanin zaɓen gwamnan jihar.

Kwamandan hukumar NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya ce jami’an za su fito ne daga rundunoni dake jihohi 10, ciki har da Oyo, Ondo, Ekiti, Ogun, Lagos, Kwara, Edo, Kogi, Delta da Abuja.

A cewar hukumar, tura jami’an na nufin tabbatar da baiwa masu kaɗa kuri’a da jami’an zaɓe da masu sa ido da ‘yan jarida da sauran mazauna jihar kariya, domin samar da yanayin da za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

NSCDC ta ce manyan jami’an ta, ciki har da Mataimakin Kwamandan Janar mai kula da ayyuka, DCG Ayuba Phillip, za su koma Osun domin sa ido da daidaita ayyukan tsaro.

Audi ya buƙaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya baya da al’ummar jihar su gudanar da kansu cikin lumana.

Yana mai cewa jami’an tsaro za su kasance masu nuna ƙwarewa da tsayawa tsaka-tsaki da mutunta haƙƙin jama’a.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaɓen ba, tare da kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani abin da suke zargin yana barazana ga tsaro ga hukumomin da suka dace.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *