Cibiyar Cibiyar Albarkatun kare Haƙƙin Ɗan Adam da da wayar da kan ‘yan Ƙasa (CHRICED) da wasu masu ruwa da tsaki sun yi kira da a ci gaba da kare asalin al’adu, tarihi da haƙƙoƙin alummamomi ’yan asalin Abuja.
Daraktan zartarwa na CHRICED, Ibrahim Zikirullahi, ne ya yi wannan kiran a ranar Litinin a Abuja, yayin wani babban taron al’adun ’yan asalin babban birnin tarayya da aka gudanar domin tunawa da Ranar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ta asalin ‘yan Ƙasa.
Zikirullahi ya ce bikin wata dama ce ta girmama ’yan asalin ƙasa a matsayin masu kula da asali, tarihi da ilimin da suka gada daga kakanninsu.
- Ya kamata a yi wa sheikh Jingir uzuri kan matsayinsa a Siyasa —Sheik Ahmad Gumi
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Gajiram
- Rundunar Sojin Najeriya takai hari kan ’Yan Bindiga Da Ke hanyar Shiga Kebbi Daga Zamfara
Ya ce yayin da Abuja ke ci gaba da zama babban birni na zamani, bai kamata a goge, rage muhimmanci ko manta da ’yan asalin garin ba.
Ya ce ya kamata a amince da harsunansu, al’adunsu, haƙƙoƙinsu na ƙasa, al’adun gargajiya da kuma gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban ƙasa, tare da mutunta su da kare su.
Shi ma Daraktan cibiyar MacArthur Foundation, Dakta Kole Shettima, ya ce gidauniyar ta shafe shekaru 32 tana tallafa wa wasu shirye-shirye a Najeriya, kuma za ta ci gaba da aiki wajen inganta haƙƙoƙin al’ummomin da aka mayar da su saniyar ware.