Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa magance matsalar rashin tsaro a Najeriya na buƙatar duba tushen matsalar, ba wai mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a yanzu kawai ba.
Gumi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce a matsayin Musulmi, akwai imani da cewa babu abin da ke faruwa a wajen ƙaddarar Allah.
Sai dai ya ce wannan imani bai kamata ya sa al’umma ta zauna ba tare da ɗaukar matakan magance abubuwan da ke haifar da rashin tsaro ba.
- Ya kamata a yi wa sheikh Jingir uzuri kan matsayinsa a Siyasa —Sheik Ahmad Gumi
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Gajiram
- NSCDC ta tura jami’an tsaro sama da dubu 10 jihar Osun
A cewar Gumi, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da matsalar shi ne sakacin da aka daɗe ana yi wajen ilimi, tarbiyya, ɗabi’a, sanin nauyin ɗan ƙasa da kuma tausayi a tsakanin al’umma.
Ya ce al’umma ba za ta iya samun kwanciyar hankali ba idan mutane da dama suka taso ba tare da samun isasshen ilimi da kyawawan ɗabi’u da ke ƙarfafa mutunta juna da zaman lafiya ba.
Gumi ya yi kira da a ƙara saka jari a fannin ilimi, tare da mai da hankali kan gina ɗabi’a, koyar da haƙƙin ɗan ƙasa da kuma cu sa tausayi a tsakanin jama’a.
Ya kuma bayyana ƙara faɗaɗar tazarar tattalin arziki a matsayin wani babban abin damuwa, yana mai cewa wasu ’yan Najeriya na fama da rashin isasshen abinci yayin da wasu ke mallakar dimbin dukiya da jiragen sama masu zaman kansu.
A cewarsa, irin wannan babban bambancin tattalin arziki na iya haifar da takaici, fushi, ƙiyayya da jin cewa an ware wasu daga cikin al’umma.
Saboda haka, ya yi kira da a samar da tattalin arzikin da zai ba ’yan ƙasa damar samun ayyukan yi da dogaro da kai, tare da rage matsanancin talauci.
Gumi ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa kasancewar gwamnati da jami’an tsaro a yankunan da ba su da isasshen kulawar gwamnati.
Ya ce wuraren da gwamnati ba ta da ƙarfi na iya zama mafaka ga masu aikata laifuka, inda suke kafa sansanoni tare da addabar al’ummomin da ke kewaye da su.
Ya bayyana ƙirƙirar ƙarin rundunonin soji na yankuna da jami’an tsaron daji a matsayin matakan da za su iya taimakawa wajen hana dazuzzuka da faɗaɗɗun yankunan karkara zama mafakar masu aikata laifuka.
Sai dai Gumi ya ce rashin tsaro ba ya samo asali daga abu guda bane, kuma ba za a iya magance matsalar da ƙarfin soja kaɗai ba.
Ya ce Najeriya na buƙatar haɗa matakan tsaro da ingantaccen ilimi, adalcin tattalin arziki, shugabanci nagari, sanin nauyin ɗan ƙasa da tausayi.
A ƙarshe, Gumi ya ce martanin Najeriya ga matsalar rashin tsaro ya kamata ya kasance mai faɗi kuma na dogon lokaci, ta hanyar haɗa ingantattun matakan tsaro da gyaran zamantakewa, samar da damar tattalin arziki, shugabanci na gari da kuma kyawawan ɗabi’u.
A cewarsa, haɗa waɗannan matakai na iya taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da sake gina amincewar jama’a ga ƙasar.