Dakarun Operation UDO KA sun kama wani shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a Jihar Enugu, tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda huɗu da harsasai 133 a wata maboyar ‘yanbindiga.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Laftanar Kanal Olabisi Olalekan Ayeni, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS.
Ayeni ya ce an kama wanda ake zargin ne a yankin Gariki na Jihar Enugu yayin wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri, bayan jami’an tsaro sun shafe lokaci suna bin sawun ƙungiyar da ake zargi da sace mutane biyu a ƙaramar hukumar Udi ranar 2 ga Agusta, 2026.
A cewar Ayeni, bayanan da aka samu daga wanda aka kama sun taimaka wajen gano shugaban ƙungiyar da ya gudu da kuma inda aka ɓoye makamansu.
Ya ce a lokacin da aka kama shi, jami’an tsaro sun kwato dala Amurka 1,000 da Naira 785,900, tare da wasu kayayyakin da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan laifuka.