Ƙungiyar Kasuwanci ta Nahiyar Afirka, AfCFTA, ta amince da tsarin zamani da Najeriya ta samar domin inganta ayyukan Kwastam, inda wani kamfanin Najeriya ya samu aikin zamanantar da harkokin Kwastam a wasu ƙasashen Afirka na tsawon shekaru 20.
Kamfanin Bergmans, ta hannun reshensa na AfriTrade CMP Limited, zai aiwatar da aikin da ya haɗa da amfani da fasahar zamani wajen bibiyar kaya da kula da iyakokin ƙasashe da inganta ayyukan Kwastam da musayar bayanan cinikayya.
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Gajiram
- Ya kamata a yi wa sheikh Jingir uzuri kan matsayinsa a Siyasa —Sheik Ahmad Gumi
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce amincewar AfCFTA da tsarin Najeriya na nuna cewa ƙasar na da damar samar da hanyoyin fasaha da za su amfani sauran ƙasashen Afirka.
Babban Sakataren AfCFTA, Wamkele Mene, ya kuma bayyana tsarin B’Odogwu, wanda Hukumar Kwastam ta Najeriya ke amfani da shi, a matsayin abin koyi ga sauran ƙasashen Afirka.
Ya ce zaɓar tsarin da kamfanonin Afirka suka samar na ƙara tabbatar da muhimmancin ƙwarewa da kirkire-kirkire daga cikin nahiyar.
Shugaba Tinubu ya ce Najeriya a shirye take ta ba da gudunmawarta wajen ganin kayayyaki na iya ratsa iyakokin ƙasashen Afirka cikin sauri, da ƙarancin kuɗi da kuma rage matsalolin cinikayya.