Kanal Mohammed Ma’aji, wanda ake zargi da hannu a wani shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce abin da ya aikata ya samo asali ne daga kishin ƙasa da kuma takaicin da yake ji kan yadda ya ce halin da ƙasar ke ciki ke ƙara tabarbarewa.

Ma’aji ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, inda ya nemi afuwa kan hannu da ake zargin yana da shi a shirin, tare da roƙon hukumomi su yi masa sassauci.

Ya jaddada cewa manufarsa ba neman wani matsayi ko biyan wata buƙata ta kansa ba ce, sai dai burin ganin Najeriya ta zama ƙasa mai inganci.

Ya ce zargin shirin ya samo asali ne daga damuwar da wasu jami’an soji ke nunawa kan yadda ake tafiyar da gwamnati, rashin tsaro, ƙarancin jin daɗin jami’an tsaro da kuma halin ƙunci da jama’a ke ciki.

A cewarsa, yanayin ya kai wani mataki da ya sa yake fargabar cewa ƙasar na iya fuskantar durƙushewa.

Ma’aji ya yi kira da a samar da wata hanya ta hukuma da jami’an soji za su iya amfani da ita wajen isar da koke-kokensu kai tsaye ga Babban Hafsan Sojin Ƙasa ba tare da fargabar fuskantar hukunci ko tsangwama ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *