Ƙungiyar Musulmi ta Duniya, tare da haɗin gwiwar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), za ta gudanar da taron tsaron ƙasa da ƙasa a Abuja, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan ƙasa da tsaro.
Taron da za a gudanar a ranar Talata, 11 ga Agusta, a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, zai haɗa malaman addini da masu tsara manufofi da sauran masu ruwa da tsaki.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce taron zai mayar da hankali kan alaƙar da ke tsakanin zaman lafiya da tsaro da bunƙasar tattalin arziki, tare da ƙarfafa fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci da sauran mabiya addinai.
- Ya kamata a yi wa sheikh Jingir uzuri kan matsayinsa a Siyasa —Sheik Ahmad Gumi
- Rundunar Sojin Najeriya takai hari kan ’Yan Bindiga Da Ke hanyar Shiga Kebbi Daga Zamfara
Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da jituwa tsakanin addinai da haɗin kan ’yan Najeriya, yana mai cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan ci gaban ƙasa.
Shi ma Babban Sakataren kungiyar Muslimi ta Duniya, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya yaba da ƙoƙarin Shugaba Tinubu na inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba.
Sheikh Al-Issa ya ce zaman lafiya a Najeriya zai taimaka matuƙa wajen ƙarfafa tsaro da kwanciyar hankali a Yammacin Afirka da ma duniya baki ɗaya.
Ministan ya kuma bayyana ziyarar Sheikh Al-Issa a matsayin wata alama ta ƙarfafa alaƙar Najeriya da Saudiyya da sauran ƙasashen duniya.