Shugaba Donald Trump ya ce Amurka tana amfani da dabarar matsin lamba ta fuskar tattalin arziki da toshe hanyoyin ruwa don ta tilasta wa Iran mika wuya a maimakon ƙara kai hare-hare.
Trump yace Iran na cikin “matsanancin hali” na Rashin kuɗi, yana buga misali da hauhawar farashin kaya da kasa biyan sojoji albashinsu.
- Iran ta gindaya sharuɗɗan buɗe Mashigar Hormuz
- Mayaƙan Houthi sun kai hari matatar man Saudiyya
- Turkiyya da Saudiyya za su gana da Firaiministan Pakistan akan Gabas ta Tsakiya
Sai dai wasu masana suna ganin ga talakawan Iran, wannan matsin ba wani sabon abu ba ne.
A cewar wakilin gidan talabijin na Aljazeera a Tehran, Tohid Asadi, wannan ba komai ba ne illa “ta-jiya, ta-jiya, wai mai amada ta manta waka”.
A cewar dan jaridar, Iraniyawa sun sha fama da wannan matsin lamba “a kwanaki ko makwanni ko ma gomman shekaru da suka gabata.”
Sai dai hakan, a cewarsa, bay a nufin ba a ji a jika a kasar ta Iran.
Hauhawar farashin kaya, da faduwar darajar kudin kasar, da kuma barazanar yaki sun jefa jama’a cikin halin ha’ula’i.
Amma duk da haka, jami’ai a kasar ta Iran suna ci gaba da nuna cewa ba za su durƙusa ba.
Yayin wani taron manema labarai, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya mayar da martani ga yadda Trump ya kwatanta lamarin da dara yana cewa ko a cikin duhu, Iraniyawa sanannu ne a matsayin ƙwararrun ‘yan wasan dara.
Bukatu shida
Iran ta gabatar da buƙatu guda shida a matsayin sharadin shiga tattaunawa, ciki har da bude hanyoyin ruwa da dakatar da hare-hare da kuma biyan diyya.
Asadi ya lura cewa waɗannan buƙatun sun yi daidai da yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla, yana nuna cewa Iran ta tsaya kai-da-fata a kan ikonta da kuma salon tattaunawarta.
Masu shiga tsakani kamar Pakistan da Oman sun taka rawa wajen ci gaba da tattaunawa, musamman a kan buɗe Mashigar Hormuz.
Amma rashin yarda da juna na ci gaba da zama matsala a mu’amalar kasashen.
Iran ta gindaya sharadin buɗe mashigin a kan janye takunkumin Amurka, ta mayar da shi wani makamin tattalin arziki da siyasa.
Wannan ya dace da muhimmiyar dabarar ta, ta jawo wa abokan gaba asara ta fuskar tattalin arziki maimakon neman nasara a fagen yaki.
Amurka ta sha mamaki
Sabanin tunanin Amurka cewa takunkumi da hare-hare za su raunana ƙarfin sojin Iran, Tehran ta nuna juriya matuƙa.
Dokta Aniseh Bassiri Tabrizi ta cibiyar Chatam House mai bicike mai zurfi a kan al’amuran duniya ta ce “zuwa yanzu, fatan Amurka cewa matsin lamba ta fuskar soji zai kifar da gwamnatin Iran, ya kuma tilasta mata mika wuya a siyasance bai tabbata ba
A cewar Doktar, Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka, tana wofintar da tunanin cewa matsin tattalin arziki kaɗai zai iya karya lagonta.
Dokta Tabrizi ta kara da cewa Iran ta yi amfani da dabarar takaita hare-hare, tana mayar da hankali a kan wuraren da za su fi haifar da tasiri ta fuskar tattalin arziki da siyasa.
A ganin wasu masana, ana iya ganin tasirin hakan a sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a game da farin jinin Shugaba Trump a Amurka, inda ake hasashen in dai ba wani sauyi aka samu nan kusa ba, jam’iyyar sa ta Republican za ta sha mummunan kaye a zabukan rabin zangon mulki da za a gudanar a bana.
Ana kukan targade…
Wasu masharhanta suna ganin sauye-sauyen shugabancin da aka sanar (inda Shugaban Kasa Masoud Pezeshkian ya ya danka jagorancin harkar tsaro a hannun Mohsen Rezaee) za su ƙara rikirkita lamarin.
Naɗin Mohsen Rezaee a matsayin Sakataren Majalisar Koli ta Tsaro ka iya zama alama ta sauyin dabarar tattaunawa.
A ganin masana irin su Muhanad Seloom, Mataimakin Farfesa a Cibiyar Ilimi Mai Zurfi ta Doha da ke Qatar, ya bayyana cewa an naɗa Rezaee ne a matsayin kan-da-garki, ga karuwar karfin fada-a-ji na Shugaban Majalisar Dokoki Mohammad Bagher Ghalibaf, kuma yana iya ƙara tsaurara matsayar Iran a tattaunawar da kasashen suke yi.
Ina aka dosa?
Trump ya dogara a kan matsin tattalin arziki ne saboda dalilai na siyasa da tattalin arziki.
Faduwar farashin mai ta rage wahalar da talakawan Amurka suke sha, ta bayar da damar ci gaba da kakaba wa Iran takunkumi ba tare da fargabar wani sakamako a cikin kasarsa ba.
Amma a ganin masharhanta da dama, tsammanin cewa wahalar tattalin arziki kaɗai za ta tilasta Iran ta mika wuya kuskure ne.
Hasali ma Iran ta nuna cewa takunkumi na iya ƙara mata ƙarfin gwiwa maimakon raunana ta.
Juriya da haƙuri sun zama ginshiƙin dabarunta, ko wanne zagaye na rikici yana ƙara mata tabbacin cewa jure wa wahala, ba mika wuya ba, shi ne hanyar tsira.
A ƙarshe, kamar yadda Dokta Tabrizi ta yi gargadi, “akwai hatsarin cewa Amurka tana fada ne da wasu hukumomin Iran da take gani a mafarkin ta ba a Zahiri ba” – ma’ana, akwai yiwuwar ita ce za ta cutu a karshe ba Iran ba.
