Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin sa na da burin ninka gudunmawar da take bayarwa ɓangaren kiwon dabbobi, daga sama da dala biliyan 32 da ake samarwa a yanzu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja yayin buɗe taron ƙasa da ƙasa karo na 9 kan kiwon dabbobi a Afirka, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilta.

Tinubu ya ce ɓangaren kiwo na taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da ayyukan yi da damar bunƙasar tattalin arziki, inda ya bayyana cewa Najeriya na da sama da Shanu miliyan 58 da Tumaki miliyan 64 da Awaki miliyan 124 da kuma Kaji sama da miliyan 660.

Ya ce gwamnati na aiwatar da shirye-shirye domin sauya harkar kiwo daga tsarin gargajiya zuwa kiwo na zamani mai amfani da fasaha, domin jerawa da kasashen duniya.

Shugaban ya ce gwamnatin sa, na shirin ƙara yawan jari a bangaren samar Madarar Nono da sarrafa nama, fatu da abincin dabbobi.

Tinubu ya ce gwamnati, na son rage dogaro da kasashen waje, domin shigo da madara, inda shirin ƙara adadin madarar da ake samar wa a cikin gida ke cigaba da fadada.

Ya ƙara da cewa harkar kiwo na da damar samar da miliyoyin ayyukan yi, musamman ga matasa da mata, ta hanyar inganta damar samun kuɗaɗen jari, fasahar zamani da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban ya kuma jaddada buƙatar haɗin kan ƙasashen Afirka wajen magance matsalolin cututtukan dabbobi da sauyin yanayi da ƙarancin abinci da matsalolin cinikayyar dabbobi da ke ƙetare iyakokin ƙasashe.

Ya ce Najeriya a shirye take ta yi aiki da sauran ƙasashen Afirka da abokan hulɗa, domin mayar da nahiyar Afirka cibiyar samar dabbobi da duniya ke bukata.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *